28 Maris 2025 - 13:30
Source: Irna
Isra'ila: An Kai Hari Da Makami Mai Linzami Daga Lebanon Kan Yankunan Da Ta Mamaye 

Hizbullah: Ba mu da hannu akai harin makami a cikin yankuna da aka mamaye 

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta lura da harba makaman roka guda biyu daga yankin Lebanon zuwa yankin Kiryat Shmona da ke yankunan da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya habarta bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na Aljazeera cewa, sojojin kasar Isra’ila sun yi ikirarin kakkabo daya daga cikin makami linzamin guda biyu inda ɗaya daga cikinsu ya fado a yankin kasar Lebanon.

A gefe guda kuma, majiyoyin labarai sun ba da rahoton cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kuma kaddamar da hare-hare kan yankunan "Kafrasir" da "Yahmar" a kudancin kasar Lebanon.

Dangane da haka, ministan yakin Isra'ila ya ce: Idan mazauna Kiryat Shmona da Galili ba su da zaman lafiya, ba za a samu zaman lafiya a Beirut ma ba.

Ya jaddada cewa: "Alhakin duk wani harin harba makami mai linzami zuwa Galili yana hannun gwamnatin Lebanon".

Isra'ila Katz, ta lura cewa Kiryat Shmona kamar Beirut ce a gare su, inda ta ce: "Ba za mu yarda a koma ranar 7 ga Oktoba (Guguwar Al-Aqsa) ba kuma za mu ba da tabbacin tsaron mazauna Galili kuma za mu yi tsayin daka kan duk wata barazana".

A cikin 'yan kwanakin nan ne dai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kara yawan hare-haren da take kai wa kauyukan Lebanon da ke kudancin kasar da Bekaa, lamarin da ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Kwanan baya, yayin wata ganawa da dan aiken shugaban kasar Faransa Jean-Henri Le Drian a fadar Baabda dake birnin Beirut, shugaban kasar Labanon Joseph Aoun ya bayyana cewa, yayin da yake ishara da halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon, ci gaba da kai hare-haren Isra'ila ya sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya-bayan nan.

Ya ci gaba da cewa: Ci gaba da mamayar tsaunuka biyar a kudancin Lebanon da Isra'ila suke yi da kuma rashin sakin fursunonin Lebanon da Isra'ila ke tsare da su ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Shugaban na Labanon ya jaddada cewa: Dole ne masu ba da tabbacin tsagaita bude wuta su matsa lamba kan Isra'ila don tabbatar da gaskiyarta, dawo da kwanciyar hankali, dakatar da hare-haren Isra'ila da tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar.

Wata majiya a cikin Hezbollah ta Lebanon ta kore hannun gwagwarmaya musulinci ta Lebanon a kan wani harin da akai yankunan da aka mamaye.

A cikin tattaunawarsa tare da tashar Almayadin, wata majiya daga Hizbullah cewa Kungiyar ta cika duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta kuma ba ta da hannun wajen kai hari a arewacin Falasdinu da aka mamaye.

Ya nanata cewa ana aiwatar da waɗannan abubuwan da suka faru don ƙirƙirar uzurin fakewa na zargi na Lebanon.

Awanni da suka wuce, gwamnatin sahyoniya ta sanar da harba makamai masu linzami biyu daga yankin Karit.

Sojojin Isra'ila sun ce sun kabo daya daga cikin makamai masu linzami kuma makami mai linzami na biyu ya sauka a Lebanon.

A gefe guda, an ba da rahoton cewa Isra'ila ta harin kai hari kan yankin Kafrair da Yahmir a Kudancin Lebanon.

Your Comment

You are replying to: .
captcha