A safiyar yau juma'a ne aka fara gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya da taken "Muna Kan Alkawarinmu Ya Qudus" a birnin Tehran da ma sauran biranen Iran inda a fadin kasar birni da kauye ake ci gaba da gudanar da jerin gwano na ranar Qudus a birane fiye da 900 da gundumomi da kauyuka da dama.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun fito kansu da kwartatarsu domin nuna goyon bayan Al'ummar Falsɗinawa tare da mayar da martani kan kin amincewa da zaluncin da Isra'ila da Amirka da sauran ƙasashe yamma suke aikatawa a Palastinu tare da rera taken "Lallai Muna Akan Alkawari Ya Qudus".
Your Comment