Rundunar Sojin sararin samaniya ta IRGC ta kaddamar da wani birni na makamai masu linzami masu inganci. Sojojin kare juyin juya hali na sararin samaniya sun kaddamar da daya daga cikin sabbin biranen makami mai linzami, wanda ke dauke da makamai masu linzami iri-iri kamar su makamin Khaibar-Shikan, Hajj Qasem, Qadr H, Sejil, Emad, da Paveh cruise missiles.
Inda Duniya tai ca akan Bullar wannan birni na Makamai mai linzami na Iran wannan Wani sako ne na dutse mai aman wuta da ke hannunka mai sanda ga kasashen Yamma. Kamfanin dillancin labaran kasar Amurka CNN ya bayar da rahoton cewa, bisa la'akari da bidiyon da aka buga aka watsa na wannan birni mai ɗauke da makamai masu linzami: Kwamandan Rundunar Sojin Sama na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana sabon birnin na makami mai linzami a matsayin "Dutsen Wuta Kwantacce". Wanda Iran ta yi amfani da wannan sansani kan Isra'ila a watan Oktoba da Afrilu".
Kamfanin dillancin labaran Sky News na kasar Amurka ya tsoma baki da cewa, yayin da yake magana kan kaddamar da wannan birni na makami mai linzami, ya kuma yi ishara da kalaman kwamandan IRGC, Birgediya Janar Hajizadeh, wanda ya ce a shekarar da ta gabata: "Idan muka fara kaddamar da birane masu makami mai linzami na Iran a kowane mako daga yau, to wadannan sansanoni ba za su kare ba nan da shekaru biyu ba".
Mujallar Newsweek ta kuma kira makamai masu linzamin da aka nuna a wannan birni masu linzami da "Gangar Fatalwa" ta kuma rubuta cewa: Wannan shi ne wuri na uku da aka bayyana cikin kasa da wata guda, wanda ke nuni da karuwar karfin sojan Iran a yayin da ake samun tashin hankali tsakaninta da Amurka da Isra'ila.
Your Comment