Gwamnatin Isra'ila ta sanya dukkan fursunonin Gaza a matsayin "masu yaki ba bisa ka'ida ba" tare da tsare su a cibiyoyin soji, inda ake azabtar da su da kuma tauye musu hakkokinsu. A shekara ta 2002, gwamnatin mamaya ta zartar da dokar “mayaki ba bisa ka’ida ba”, wadda ta bai wa sojoji damar tsare Falasdinawa ba tare da tuhuma ko shari’a ta gaskiya ba, bisa dogaro da “fayil din sirri” kawai!
Tun daga 2005, wannan doka ta zama kayan aiki don murkushe mazauna Gaza, kuma ba a ba su 'yancin yin wata zanga-zanga ko bitar shari'a ba!
A yakin kisan kiyashi da take ci gaba da yi a zirin Gaza, ta kama dubban mazauna Gaza bisa ga wannan doka, kuma ba a san makomar yawancinsu ba kuma babu tabbas a rayuwarsu!
Inda bisa wannan doka aka canza matsayin Dakta Hussam Abu Safiyya zuwa “Mai Yaki ba bisa ka’ida ba” wanda Cibiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Meezan ta sanar da cewa, halin da ake ciki na tsare Dakta Hussam Abu Safiya, darektan Asibitin Kamal Adwan da ke Gaza, an canza shi zuwa “mai yaki ba bisa doka ba.
cibiyar kare hakkin bil adama ta Mizan ta sanar da cewa, bisa umarnin Yaron Finkelman, kwamandan yankin kudancin haramtacciyar kasar Isra'ila, Dr. Hussam Abu Safiya, darektan asibitin Kamal Adwan da ke arewacin zirin Gaza, ana tsare da shi ne bisa dalilan cewa shi "mai yaki ne ba bisa doka ba"
Lauyan Cibiyar Mizan ya bayyana cewa Dr. Abu Safiya an gallaza masa da cin zarafinsa.
Cibiyar ta kara da cewa mutanen da ake tsare da su a karkashin dokar mayakan da ba bisa ka’ida ba, an tauye musu hakkin sanar da su tuhume-tuhumen da ake tuhumar su da su, da kuma ‘yancin yin nazari kan hujjojin da ake tuhumar su da su, domin su samu ikon kare kansu.
Cibiyar ta Mizan ta jaddada cewa mayar da matsayin Dr. Abu Safiya zuwa "mayaki ba bisa ka'ida ba" mataki ne na son rai, dake da hadari, kuma matakin bita da kulli ne, kuma yana nuni da gazawar masu shigar da kara na Isra'ila wajen tabbatar da ikirarin da ake yi masa.
Cibiyar ta yi kira ga kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakan da suka dace don ganin an sako Abu Safiya da sauran jami’an lafiya da na agaji cikin gaggawa.
A ranar 28 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da kame Abu Safiya da sojojin Isra'ila suka yi. Kafin haka dai sojojin gwamnatin sun afkawa asibitin Kamal Udwan inda suka kona shi gaba ɗayansa.
Your Comment