Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarto bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na Ansarullah cewa, dakarun kasar Yemen sun kara da cewa, a matsayin mai da martani ga hare-haren da Amurka ta kai wanda ya dace da bikin cika shekaru 10 na ranar jajircewar kasar a ranar 26 ga watan Maris, bisa tsarin fuskantar gaba da gaba a cikin tsarin daukar fansa, makami mai linzami na Yemen, da jiragen yaki marassa matuki, da sojojin ruwa na kasar Yemen, sun kai hari kan jirgin Truman da wasu jiragen yakin Amurka a tekun Bahar Rum, a cikin sa'o'i kadan da suka kaddamar da farmakin hadin gwiwa a kasar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, an dauki tsawon sa'o'i da dama ana gwabzawa, kuma har ya zuwa lokacin da aka sanar da wannan sanarwa, sojojin kasar Yemen na ci gaba da tunkarar hare-hare yadda ya kamata tare da tunkarar al'amura daban-daban da kuma abubuwan da suka faru a yankin da suke gudanar da ayyukansu.
Sanarwar da Rundunar Sojin Yaman ta fitar ta bayyana cewa, domin kare hakkin al'ummar Palastinu a Gaza da kuma ci gaba da ba su goyon baya da kuma mara musu baya, a baya sojojin gwamnatin Yamen sun kai hari kan wuraren da sojojin yahudawan sahyoniyawa suke a yankin Jaffa da suka mamaye da jirage masu saukar ungulu da dama, kuma cikin ikon Allah an cimma nasarar cimma manufar wannan farmakin.
A cikin sanarwar da ta fitar, Rundunar Sojin Yaman ta jaddada ci gaba da tinkarar hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa, da kuma ci gaba da hana zirga-zirgar jiragen ruwan haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin da aka ayyana, tare da ci gaba da kai hare-hare kan makiya yahudawan sahyoniya har sai sun daina kai hare-hare a zirin Gaza.
Dakarun Yaman sun yi kira ga dukkanin al'ummar musulmi masu 'yanci da su dauki matakin dakile laifukan kisan kiyashi da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa al'ummar Zirin Gaza.
Bayan sake kai hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza, sojojin Yaman sun ci gaba da kai hare-haren soji da makamai masu linzami kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, domin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da ake zalunta.
A baya dai shugaban kungiyar Ansarullah ta Yaman ya baiwa masu shiga tsakani wa'adin kwanaki hudu, yana mai cewa idan ba a bari an kai agajin jin kai a Gaza ba, to sojojin ruwan Yaman za su ci gaba da kai farmakin kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Dangane da haka Sayyid Abdul Malik Badruddin Al-Houthi jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya sanar a ranar 12 ga watan Maris din shekara ta 2025 cewa yunƙurin hana ratsawar jiragen ruwa da ke da alaka da gwamnatin sahyoniyawa ta cikin tekun Bahar Maliya, Babul-Mandab, mashigar tekun Aden, da tekun Larabawa ya shiga matakin aiwatarwa.
Jagoran kungiyar Ansarullah ya jaddada cewa matukar ba a kawo karshen hare-haren da aka kai wa zirin Gaza ba, to za mu yi amfani da dukkan hanyoyin da za mu bi wajen tunkarar matsalar yunwa da al'ummar Palastinu ke ciki.
A halin da ake ciki dai kasashen Amurka da Birtaniya da ke goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan sun kaddamar da hare-hare ta sama kan kasar Yemen a ranar 15 ga watan Maris din shekara ta 2025, inda suka kai hare-hare a wuraren zama da cibiyoyin fararen hula a kasar.
Your Comment