Yara 15 daga zirin Gaza sun mutu sakamakon tsananin sanyi da ya addabi yankin kwanan nan. Asibitocin Gaza, musamman ma wuraren kula da kananan yara, ba sa iya jurewa yanayi mai tsanani da sanyi ke haifarwa, saboda ko dai an lalata su da hare-haren mamaya ko kuma an lalata kayan aiki da kayayyakin da ke cikin su.
Gwamnatin mamaya ba ta bi ka'idojin jin kai ba da aka sanya akai yarjejeniya ba, gami da shigo da kayan aikin likita, kayan dumama yanayi, tantuna, da gidaje na wucin gadi.
