25 Faburairu 2025 - 19:36
Mutane Dubu 4.500 Ne Suka Rasa Wata Gaɓa Daga Jikinsu Sakamakon Hare-Haren Isra'ila A Gaza

Wandanda Aka Yankewa Wata Gaɓa Ta Jikinsu 4,500 Ne A Gaza Ke Jiran Ayi Masu Magani Sakamakon Laifukan Ta'addancin Isra'ila Na Hare-haren Da Ta Ke Kaiwa

Wandanda Aka Yankewa Wata Gaɓa Ta Jikinsu 4,500 Ne A Gaza Ke Jiran Ayi Masu Magani Sakamakon Laifukan Ta'addancin Isra'ila Na Hare-haren Da Ta Ke Kaiwa

A wani rahoto da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta fitar, adadin mutanen da aka yankewa wata gaɓa daga jikinsu tun farkon fara yakin ya kai kimanin 4,500, daga cikinsu akwai 1,302 da suka hada da maza 1,041 da mata 261 a hukumance.

A halin da ake ciki, yaran da aka yankewa wata gaɓa daga jikinsu sun kai kashi 15 cikin 100 na wannan adadi, kuma kashi 83 cikin 100 na yankewar suna cikin ƙananan gaɓoɓin yara ne.

Akwai kuma mutane 14,500 da suka samu munanan raunuka da ke bukatar gyara da ɗori na dogon lokaci, yayin da asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya ke fuskantar karancin kayan aikin likita da magunguna.