14 Faburairu 2025 - 12:21
Hamas Gobe Za Ta Saki Fursunonin Isra'ila Uku

Kamar yadda Abu Ubaidah, kakakin Al-Qassam ya fada cewa za a saki fursunonin yahudawan sahyoniya 3 a gobe.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (ABNA) sun kawo maku rahoton aci gaba da gudanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunonin tsakanin Hamas da Isra'ila, Gwagwarmaya ta ce ba za ta saki fursunonin ba idan ba a cika sharuddan tsagaita bude wuta ba. Wannan barazana ta sa yahudawan sahyuniya suka mika wuya ga Hamas, wanda da hakan za'a saki fursunonin uku a ranar Asabar.

Fursunonin Palasdinawa 369 ne aka saki a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni

Gwamnatin Isra'ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 369 a gobe Asabar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni da 'yan adawa a Gaza.

36 daga cikin wadannan fursunoni an yanke musu hukuncin daurin rai da rai, kuma fursunoni 333 mazauna zirin Gaza ne da aka kama a yakin kisan kare dangi na baya-bayan nan.