An fara tsagaita wuta a Gaza a hukumance
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin ‘yan adawa da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta fara aiki a hukumance daga wannan minti.
Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa za su ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza.
Kakakin sojojin mamaya ya jaddada cewa sojojin sun yi ruwan bama-bamai a arewaci da tsakiyar zirin Gaza tare da kai musu hare-hare da bindigogi.
Falasdinawa 8 Sun Yi shahada Bayan An Fara Tsagaita Buɗe Wuta A Hukumance
Majiyar labaran Falasdinu ta fitar da rahoton shahadar Palasdinawa 8 tare da jikkata wasu da dama a wani harin Yahudawa yan mamaya da aka kai a unguwar Al-Sha'af da ke gabashin birnin Gaza.
bayan nan adadin wadanda sukai shahada sakamakon harin bam a Gaza ya karu zuwa 5
Majiyoyin kiwon lafiya sun sanar da cewa adadin shahidan da suka yi shahada a harin bam din da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a unguwar Al-Sha'af da ke birnin Gaza ya karu zuwa mutane 8 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai 20.
Majiyar Hamas: Za a saki mayakan Hezbollah na Lebanon a mataki na biyu na tsagaita wuta
A cewar wata majiya daga kungiyar Hamas, za a saki dukkan fursunonin da sojojin Isra'ila suka tsare bayan ranar 7 ga watan Oktoba, ciki har da mayakan Hizbullah na kasar Labanon, a mataki na biyu na tsagaita bude wuta.
Sahyoniya suna ci gaba da neman karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta
A yayin da tsagaita wutar ke aiki a zirin Gaza tun daga karfe 8:30 agogon birnin Kudus wato karfe 10:00 na Tehran, sojojin Isra'ila sun yi niyyar karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da nufin ba a mika sunayen fursunonin ba.
Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da wata sanarwa inda ta sanar da cewa ba ta samu jerin sunayen fursunonin ba, kuma ba za a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba har sai Hamas ta cika hakkokinta. Sojojin Isra'ila sun jaddada cewa za su ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza.
