23 Disamba 2024 - 18:32
Jami'an Tsaron Najeriya Sun Kama Mabiya Sheikh Ibrahim Alzakzaky A Abuja

Duk da Ƙarar da Almajiran Malam Zakzaky Suka yi a Kotu, Yan Sanda Sun Kama Sama da Mutane 200 a Wajen Taronsu a Abuja

Sama da mutane dari biyu ne da suka hada da jarirai da mata masu ciki da kananan yara hukumar yan sandan Najeriya suka kama a yayin da mabiya mazhbar Shi'a Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky suka gudanar da taron tunawa da ranar Haihuwar Ƴar Manzon Allah, Sayyida Fatima Azzahara a Abuja.

Taron wanda ya dauki tsawon kwanaki uku suna gudanarwa kamar yanda wata majiya ta shaida wa jaridar Sahara Reporters.

Sai dai a yayin da suka hadu domin rufe taron yan sanda sun hallara bayan kammalawa sun kame sama da mutane dari biyu, lamarin kamun dai ya faru ba tare da an harbi kowa ba.

Har zuwa haɗa wannan rahoton dai yayan Harkar Musuluncin basu san adadin wadanda aka kama musu ba, su kuma yan sanda basu bayyana adadin mutanen da suka kama ba.

A makon da ya gabata ne dai yan Harkar Musuluncin suka garzaya kotu sun neman diyya kimanin Naira Miliyan dari biyu daga wajen Gwamnati da hukumar yan sanda saboda gallaza musu da ake yi a yayin gudanar da taron addinin da suka saba yi tsawon shekaru a Abuja.