21 Disamba 2024 - 19:04
Taya Murna Da Haihuwar Shugabar Matayen Duniya Da Lahira Sayyidah Fatimah As

Sayyidah Fatimah Salamullahi Alaiha Wa’abiha Ba’alaha Wa Baniha Wasirril Musatauda’u Fiha Diyar Manzon Allah Daga Sayyidah Khadijah Alaihassalam An Haifeta A 20 Ga Jumadal Akhir Shekarata Biyar Bayan Aiko Annabi Salamullahai Alaihin Wa’alihi.

    Sayyidah Fatimah Salamullahi Alaiha Wa’abiha Ba’alaha Wa Baniha Wasirril Musatauda’u Fiha Diyar Manzon Allah Daga Sayyidah Khadijah Alaihassalam An Haifeta A 20 Ga Jumadal Akhir Shekarata Biyar Bayan Aiko Annabi Salamullahai Alaihin Wa’alihi.

Ita Ce Shugabar Matan Duka Duniya Da Lahira Mahaifiya Ga Shugabannin Samarin Aljannah Imam Hasan Da Husain As Diyar Mafificin Halitta Cikamakon Annabawa Wanda Allah Yafi So Cikin Gabaki Dayan Halittarsa.

Ana Mata Alkunya Da Ummu Abiha Ummul Hasanain Ummul Sibdain Ummul A Immah Anamataa Lakabi Da Siddikah Kubrah Batul Dahira Sayyidati Nisail Alamiin’ Mudahhara Radiyah Mardiyyah Suna Daga Cikin Lakubbanta.

Itace Wadda Allah Subhanau Wata’ala Ke Yarda Da Yardarta Yake Fushi Da Yin Fushin Ta. Manzan Allah Yana Cewa Fatimah Tsokar Jikina Ce Wanda Duk Ya Fusata Ta To Ni Ya Fusata.

Sayyidah Fatimah As Tabar Mana Abinda Muke Tunawa Da Ita Ako Da Yaushe Bayan Sallar Mu Waton Tasbihuzzahra’a Wanda Mu Keyi Duk Bayan Sallah’ wato Subhanallahi Walhamdulillah Allahu Akbar.

Haihuwar Sayyida Fatmah {S}

            Sayyidah Khadija {S} Tana Cewa: Yayin Da Na Dauki Cikin  Sayyidah Fatimah {S} Cikina Ya Kasance Maras Nauyi, Kuma Ta Kasance Tana Zantar Dani Tun Tana Cikina, Ma’ana Munayin Hira Da’ita Yayin Da Haihuwarta Ta Gabato Wadansu Mata Kyawawa Wanda Kyawunsu Baya Misaltuwa, Sun Shigo Wajena Su Hudu: Tafarkon Ta Ce Nice Babarki Hawwa’u {S} Tabiyu Ta Ce Ni Ce Asiya Yar Muzahim, Ta Ukku Ta Ce Ni Ce Kulsum Yar Uwar Musa {S} Taqarshe Ta Ce Ni Ce Maryam Yar Imrana {S} Mahaifiyar Isah {S} Mun Zo Ne Domin Karbar Abin Haihuwarki Sai Ta Haifi Sayyadah Zahara {S} BIsa Kulawar Wadannan Bayin Allah Tsarkaka Da Ya Zaba. Sayyidah Fatimah An Haife Tane Tana Mai Sujjad A Ranar Ashirin Ga Watan Jumadal Akir Shekara Ta Arba’in Da Biyar Bayan Haihuwar Manzon Rahama {S} Bayan Aiko Manzon Allah Da Shekara Biyar, Kuma Quraishawa Suna Gina Dakin Ka’abah. Shekarunta Tare Da Mahaifinta A Makkah 8 A Madina 10 Tare Da Imam Aliyu Bayan Wafatin Mahaifinta Kwana 75 Ko 40.

            An Karbo Daga Mufaddil Bin Umar {R} Cewa Ya Tambayi Imamuss-Sadiq {A} Yaya Haihuwar Sayyadah Fatimah {S} Ya Kasance? Sai Yace: { Na’am Lallai Sayyidah Khadijah Yayin Da Ta Auri Manzon Allah {S} Matan Quraishawa Sun Qaurace Mata Basa Shiga Gidanta Basa Yi Mata Sallama Kuma Basa Barin Wata Mace Ma Tashiga Gidanta, To Sai Sayyidah Khadijah Ta Damu Dangane Da Hakan, Bayan Ta Dauki Cikin Sayyidah Fatimah, Sai Ta Kasance Suna Magana Da Ita Tun Tana Cikinta, Tana Bata Haquri Akan Abunda Matan Quraishawa Suke Mata, Sayyidah Khadijah Ta Kasance Tana Boye Wannan Hirar Da Suke Yi Da Diyarta, Har Saida Wata Rana Manzon Rahama {S} Ya Shigo Yaji Sayyidah Khadija Tana Magana Da Sayyidah Fatimah {S}  Saiyace Da’ita: Yakhadijah Wake Magana Dake ? Sai Tace: Jarin Dake Cikina Shike Magana Dani Mukeyin Hira,  Sai Yace Da Ita Ga Mala’ika Jibrilu {S} Nan Yana Min Bushara Cewa Lallai Maca Ce Tsarkakakkiya, Kuma Allah Tabaraka Wata’ala Zai Sanya Tsatona Daga Wajanta Kuma Zai Sanya Daga Tsatsonta Shugabanni A Wannan Al’ummar Ya Sanya Su Halifofi A Doran Qasar Sa Bayan Yankewar Wahayinsa.

Darajojinta:

1- Shugabar Matan Duniya Da Lahira.

2- Diyar Manzon Rahama Wanda Babu Tamka Tasa Duniya Da Lahira.

3- Matar Imam Ali {S} Wanda Yake Annabwa Suke Kabar Karatu Tawajansa Kuma Da Shine Allah Ya Ke Taimakon Su. Wajan Isar Da Saqonsa.

4- Mahaifiyar Shugabannin Aljannah Da Kuma Duniya Da Lahira.

5- Wacce Aka Daura Auran Ta A Sama Da Kwana Arba’in Kana Aka Daura A Qasa Da Sadaki Dirhami 480. Tana Shekara Tara.

6- Wacce Allah {S} Keyin Fushi Da Fushinta Yake Yarda Da Yardarta.

7- Ita Ce Wacce Aka Sherawa Manzon Allah Damuwa Da Tsangwama Da Haihuwarta.

8- Wacce Allah {S] Yabada Auranta, Mala’ika Jibrilu {S} Manemin Auranta, Mala’ika Maika’il Da Israfil {S} Da Mala’iku Dubu Saba’in Sune Shaidar Daurin Aurenta.

9- Itace Yar’ Annabi, Matar Imam Ali {S] Mahaifiyar A’immah {S}.

10- Itace Wacce Allah Zai Fara Yin Hukunci Ga Wadan Da Suka Zalunce Ta Da Ya’ayanta.