Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul Bayt (AS) – ABNA – ya kawo maku rahoton cewa: An fara gudanar
da taron horon aikin jarida na kasa da kasa kan "Harkokin Yada Labarai a
fagagen kasa da kasa" kafin azahar din yau Juma'a 20 ga watan Disamba
2024, karkashin jagorancin Kamfanin Dillancin Labaran Ahlul Baiti (a.s) A) na
Duniya - Abna - a zauren taron na wannan kamfanin dake a birnin Qum.
Wannan kwas din ya samu halarta da jawabin “Dr Suhail As’ad” da "Hasan Sadraei Aref" da “Hasan Shamshady” da “Murtadha Gharqy” da “Muhammad Qadiry” da “Mardhiyyah Hashimy” da “Dr Ilham Abidy” da “Ilham Shakiry”.
A wajen bude kwas din, Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Abna Hasan Sadraei Aref, ya yi nuni da muhimmancin kafafen yada labarai, ya kuma bayyana cewa: Kafafen yada labarai su ne ginshikin yaki da fagensa ne, kuma a yanzu kafafen yada labarai sun kai kololuwar matsayin da suke da shi wajen yin tasiri Don haka, ya kamata mu kasance da masaniya game da ci gaban kafofin watsa labarai kuma mu iya yin aikin watsa labarai da kanmu a fagen duniya. Dangane da haka ne kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (A.S) ya shirya gudanar da wani kwas na horas da aikin jarida na kasa da kasa mai taken ''fasahar yada labarai a fadin kasa da kasa''.
Ya ci gaba da cewa: A cikin kwas din aikin jarida na kasa da kasa, an yi amfani da shahararrun malamai da kwararru, kuma gudanar da wannan kwas zai zama kyakkyawan mataki na farko ga kwasa-kwasai na gaba mai taken aikin jarida na kasa da kasa.
Babban daraktan kamfanin dillancin labarai na Abna ya kara da cewa: Haka nan saboda bukatun masu saurare muna shirin gudanar da wani kwas domin amsa dukkan shubuhohi da kuma kare mazhabar Ahlul Baiti (AS) a fagen kasa da kasa ta fuskar tsarin koyarwar addinin musulunci kafofin watsa labarai. Waɗannan kwasa-kwasan horon tushe ne na ƙarfafa kafofin watsa labarai a fage na duniya.
Sadraei Aref ya yi nuni da cewa: Mun ga yadda akai tarba da karba mai kyau ga kwas din aikin jarida na kasa da kasa duk da cewa ba a ba da sanarwar wannan kwas din ba, kusan mutane 300 ne suka yi rajista don shiga wannan kwas, kuma a karshe mutane 70 daga kasashe 5 ne suka halarci kwas din a cikin tsarin halarta kaitsaye da wadanda suka halarta daga nesa.
.................................