Muhimmiyar hanya ta sanin wacce ta kafa tarihi kamar Fatimah (a.s.) ita ce sanin yanayin zamantakewar da aka haifi da tasowar Fatimah (a.s.) a cikinta. Fatima (A.S) a cikin mutane tana daga cikin iyalan Ibrahim, kuma a cikin iyalan Ibrahim, tana daga iyalan Ismail, kuma daga cikin iyalan Ismail, tana daga Bani Hashim, kuma daga cikin Bani Hashim din tana daga cikin wadanda suka zabi tsarin halitta na dabi’ah ne wanda ta tabbata bisa gadon Ibrahim, wanda ya kasance abun ke jagaba a gadon Ibrahim shine imani da tauhidi da kuma aiki da addinin Hanif na Ibrahim, kuma daga cikinsu tana daga cikin Ahlul Baitin Annabi karshen Annabawa (AS), kuma a cikin Ahlulbaitin Manzon Allah (AS), ita ce kadai ‘yar Manzon Allah (SAW) wanda bayansa ta rayu na wani dan kankanin lokaci, kuma a cikin kankanin lokaci, ta katse shirun da ya mamaye Madina ta tsayu da daga tutar nuna adawa da abin da Larabawa suka yi, kuma ta yi haka, alhali kuwa an riga an tabbatar da ita a matsayin mai banbance tare da nuna shiriya da bata daga bakin Annabi kuma ya bayyana karara cewa cutar da ita cutarwa ce ga Allah da Manzonsa (SAW).
Fatimah (AS) A Matsayinta Na Farkon Wacce Ta Nuna Adawa Da Juya Bayan Larabawa.
Yana da muhimmanci a ce Fatimah (AS) ta ki amincewa da juya bayan Larabawa, amma abu mafi muhimmanci da wannan ma shi ne Fatima (AS) ita ce ta farko data zamo mai adawa da juya bayan Larabawa da kaucewarsu ga siyasa tsarin Imamanci zuwa ga anfani da tsarin siyasa na halifanci (57) wanda daga karshe ya kai ga dawowar daular da farfado da dukkanin yanayin zamantakewa da suka dace da tsarin baya. A wani yanayi da ya zamo dukkan manyan ‘yan siyasa suka yi shiru ba wanda ya kare Imam da Imamanci da dukkan karfinsa, Fatimah (a.s) ta sadaukar da kanta wajen kare Imam da Imamanci har ya kai ta samun shahada a irin wannan tafarki, kuma hakan da Fatima tayi na sadaukar da kanta, ya kasance babban abin alfahari a gare ta, kuma ya zamo darasi mai girma a garemu.
Har Yanzu Ba A Iya Rufe Lamarin Rayuwar Fatimah Da Rasuwarta Ba:
Rayuwa da wafatin Sayyidah Fatima (a.s) bayan Manzon Allah (s.a.w.s.) duk sun kasance cikakkun madubin gwagwarmaya da ta yi na nuna adawa da matakin juya baya da Larabawa suka yi. Bayan Manzon Allah (SAW) Fatima (a.s) ta kasance har karshen rayuwarta mai “Tawaye” ce kan juya bayan da Larabawa suka yi. Ba ta tsaya guri daya ba kuma bata daina nuna rashin amincewa da juya bayan Larabawa ba. Ta yi fatan dukkanin masu juyin juya halin Musulmai zamaninta da su tashi tsaye wajen daukar tutar kare hakikanin sakon da Manzon Allah (SAW) ya zo da shi da kuma kare tsarin siyasar Imamanci da dukkan karfinsu ba tare da la’akari da tsananin hanyoyin mayar da martani na masu juya baya, sannan su nesantar da al’ummar musulmi daga dukkan tarkon masu juya baya da dukkan bangarorinta na kariyar Kuraishawa ne ko na jari hujja, ko a cikin rigar kishin kasa na Larabawa da kabilanci da girman kai na kasa, ko cikin rigar son duniya na banu Umayyawa, ko na rigar munafuncin Abbasiyawa da masu neman samun damarmaki, ko na cikin wata riga ta daban a ko wane lokaci. Saboda haka har yanzu Fatimah (AS) tana jiran al'ummomin da suka ci gaba a cikin al'ummar bil'adama su bada amsa mai kyau ga kiran muryarta na kin amincewarta da wannan tsarin. Su kuma bada kariya ga ginshikan da Annabci ya kafa da haqiqanin saqo da gadon da Ma’aiki (SAW) ya bari da cibiyar Imamanci da isar da sakon Imam da hakkokin al’umma. Boyuwar kabarin Sayyidah Fatimah (AS) a tarihi yana nufin ci gaba da yunkurinta da kuma alamar kin yardarta da ya faru a tarihi ne, kuma wannan kin amincewa za ta kare ne a lokacin da rayuwar tsarin sarauta da na kama karya yazo karshe a duniyar Musulunci, sannan kuma tsarin Imamanci na Muhammadiyya ya samu farfadowa tun daga farko da kuma samuwar tabbatarsa, ta yadda al'ummar duniya za ta ginu a kan tsarin Alkur'ani, don tabbatar da manufa ta siyasa na duniyar da ba ta da bayi da kasar da ba ta da hamada da faqo, da kuma samar da duniyar da babu talaka a cikinta.