20 Oktoba 2024 - 07:42
Harin Da Aka Yi A Amurka Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 3 Da Jikkata 8

Rahotanni daga kasar Amurka na nuni da cewa mutane 3 ne suka mutu kana wasu 8 suka jikkata sakamakon harbin da aka yi a yayin bikin cin nasara na wasan kwallon kafa a tsakiyar birnin Mississippi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na Associated Press ya nakalto cewa, a yau Lahadi, daga jami’an kasar cewa: A wannan harbin da aka yi a safiyar ranar Asabar, akalla mutane biyu ne sukai harbi a wani gungun mutane sama da dari da suke murnar samun nasara a wasan kwallon kafa na makarantar wasa a fili.

Harbin ya faru ne bayan da aka buga wasan kwallon kafa kuma mutane da dama bayan wasan sun yi ta rigima, amma a cewar ‘yan sandan yankin Holmes a Mississippi, ba a san abin da ya haddasa fadan ba.

Rundunar ‘yan sandan yankin ta tabbatar a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa mutane 200 zuwa 300 ne ke murna a wajen inda bayan harbin bindigar suka tarwatse.

Biyu daga cikin wadanda wannan harin na harbin bindiga ya rutsa da su matasa ne 'yan shekara 19, sannan na ukun dan shekara 25 ne, kuma an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Yin amfani da bindigogi da harbe-harbe a Amurka ya zama matsala a kasar, musamman a gundumar Holmes, mai yawan jama'a kusan 16,000, hakan na faruwa a kowane lokaci.

A cewar IRNA, an sami karuwar laifuka da tashe-tashen hankula da makamai ke haddasawa a Amurka a cikin 'yan shekarun nan.

Cibiyar Rikicin Ta'addanci (GVA) a baya ta sanar da cewa a cikin 2023, fiye da mutane 42,000 a Amurka suka mutu da harbin bindigogi.

A daya bangaren kuma, hukumar ‘yan sandan tarayya ta Amurka (FBI) ta bayar da rahoton karuwar ta’addanci a makarantu da jami’o’in kasar.

A cewar rahoton, daya daga cikin 10 na laifuka da tashe-tashen hankula a kasar yana faruwa ne a makarantu ko jami'o'i. Rahoton ya yi iƙirarin cewa akasarin waɗanda waɗannan laifuffuka suka shafa baƙaƙe ne da kuma Yahudawa dalibai.