Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: an gudanar da taro karo na
194 na majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-baiti As, a ranar Alhamis 17
ga Oktoba, 2024 a birnin Qum, kuma A karshen wannan taro, 'yan majalisar koli
na majalisar sun bayyana ra'ayoyinsu kan muhimman al'amuran da suka shafi duniyar
musulmi, da Shi’a a matsayin bayani na karshe na wannan taro.
Matanin wannan bayanin yazo kamar haka:
بسم الله الرحمن الرحیم
قال الله تعالی: إِنَّ اللَّهَ يُدَافِعُ عَنِ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ خَوَّانٍ كَفُورٍ
Da sunan Allah, Mai rahama Mai jinkai
Allah Ta’ala ya ce: Lallai Allah yana bada kariya ga wadanda suka yi Imani Lalle Allah bay a son dukkan mai ha’inci mai kafircewa.
An gudanar da taro na dari da casa’in da hudu na majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, a kusa da harami mai albarka na Karimatu Ahlul-baiti mai tsarki a birnin ilimi da jihadi da ijtihadi a wani yanayi da duniyar musulunci ta shaida yadda ake ci gaba da yaki tsakanin gaskiya da karya tare da gwagwarmaya da jarumtakar al'ummar musulmin Palastinu da Lebanon da kuma munanan laifuka na gwamnatin sahyoniya da kuma shahadantarwa bisa ga zalunta ta shahadar shugaban gwagwarmaya, jagoran 'yantar da Quds Sharif alkibla ta farko ta musulmi kuma fitaccen mamba a majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su. Allamah Mujahid, Sayyid Hujjatul Islam wal muslimin, Sayyid Hasan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da kuma Wasu daga cikin abokansa da kwamandojin Hizbullah bayan shahadar Mujahid Kabir kuma shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Falasdinawa Hamas, Shahidai Ismail Haniyah da mayakan kungiyoyin gwagwarmaya a Gaza, a yayin tunawa da zagayowar nasarar tarihi na guguwar Al-Aqsa.
A cikin wannan taro, baya ga batutuwan da suka shafi kungiyoyi, an tattauna sabbin abubuwan da suka faru a yankin tare da halartar 'yan majalisar da manyan baki, daga karshe mambobin majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-Baiti As, sun bayyana matsayinsu kamar haka:
1. Shahada da rasa jagora balarabe na gwagwarmayar Musulunci, Allamah Mujahid, Sayyid Hasan Nasrallah, ya kasance babban abin bakin ciki da takaicin al'ummar musulmi. Sayyidush Shuhada na gwagwarmaya ya kasance jagoran gwagwarmaya mai jajirtacce wajen gwagwarmaya a tsawon shekaru talatin kuma ya sami damar inganta kungiyar Hizbullah da gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon da kuma yankin mataki bayan mataki. Kokarin da ya yi na karfafa matsayin mabiya Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, tare da jaddada hadin kan al'ummar musulmi, ya samar da wata bishiya mai kyau wacce dukkanin musulmi, har ma da 'yantattu na duniya, za su amfana a ko da yaushe daga albarkatunta. Kokarin Alamah Mujahid Sayyid Hasan Nasrallah a matsayinsa na fitaccen memba a majalisar koli ta Ahlul-Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, da sadaukar da kai ga al'amuran al'ummar musulmi, akan gaba da dukkaninsu lamarin Palastinu. sannan kuma da irin rawar da ya taka wajen inganta addinin muslunci na Muhammadiyya da mazhabar Ahlulbaiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, ya zama abin koyi ne ga dukkan ma’abota alaka da Ahlulbaiti (amincin Allah ya tabbata a gare su).
2. Bisa ga kulawa da jagoranci da umarni mai cike da hikima na jagoran juyin juya halin Musulunci mai hikima Ayatullah Uzma, Imam Ali Khamenei Maddzilluhu Ali dangane da muhimmancin ci bunkasa da kuma kara himma ga ci gaba da gudanar da ayyuka bayan shahadar Sayyid Shuhada na gwagwarmaya da kuma tabbatarwar Jagora ga wajabcin wanzar da hadin kan musulmi domin samun daukaka da kuma shawo kan matsalolin da suke fuskantowa. Mambobin majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, sun yi la'akari da wadannan bayanai a matsayin taswirar hanya ga al'ummar musulmi, musamman mabiya tafarkin Ahlul-baiti, don ci gaba da gwagwarmaya wajen fuskantar shirin Amurka da sahyoniyawan da kuma yin tsayin daka wajen yakar laifukan gwamnatin mamaya ta Qudus a cikin yankin’ Suna bayyana cikakken kudurinsu na ci gaba da kokarin tabbatar da wadannan ka'idoji da kuma jaddada hadin kan Musulunci da hadin gwiwa da aiki tare da dukkan 'yan Shi'a a duniya.
3. Majalisar koli ta Ahlul-Baiti ta duniya ta bayyana jin dadin ta da irin matsayin da maraji’an Shi'a suke da shi na tsawon lokaci a Hauzozin Qum, Najaf da sauran kasashen musulmi, musamman ma maraja’i mai hikima da hangen nesa na Ayatullah Uzma Sayyid Sistani Maddzilluhul Aali cikin dukkanin goyon bayan da yake bayarwa ga wadanda ake zalunta a Gaza da Lebanon da kuma bayyana matsayarsu na yin Allah wadai da gwamnatin sahyoniya.
4. Mummunan ayyukan gwamnatin sahyoniyawa da laifukan da take aikatawa kan bayin Allah da garuruwa, da suka hada da kashe mutane bisa zalunci, musamman mata da kananan yara a Gaza da Lebanon, wanda ke faruwa a karkashin inuwar ma'abota girman kan duniya da Amurka ke jagoranta wannan na nuna babban yaudarar wayewar yammacin duniya a ko da yaushe har bayan yakin duniya na biyu da ke riya 'yancin ɗan adam, dokokin kasa da kasa da hanyoyin da haƙƙin ɗan adam a lokacin rikice-rikice na makamai. Majalisar kolin duniya ta Ahlul-Baiti, amincin Allah ya tabbata a gare su, ta yi kakkausar suka ga laifukan wannan gwamnati da ke da goyon bayan Amurka da yin shurun shugabannin wayewar kasashen yamma, duk kuwa da samun gagarumin sauyin ra'ayin jama'a na duniya, Ta kuma jaddada cewa wadannan goyon baya na gaba daya da kuma matsayin yaudarwa na fuska biyu na kasashen yamma, tare da taimakon Allah a kan ikon Allah da azamar dakarun za su sha kaye, kuma ba za su iya kubutar da wannan muguwar gwamnati ba daga halin kakanakayi da take ciki kuma insha Allah nan ba da jimawa ba za ta kai ga rugujewa.
5. Mambobin majalisar koli ta majalisar sun jaddada cewa a halin da ake ciki, abin da kasashen musulmi suka sanya a gaba shi ne tallafawa al'ummar Palastinu da Lebanon da ake zalunta. Majalisar kolin Duniya ta Ahlul-Baiti ta bukaci daukacin al'ummar duniya masu 'yanci cikin wannan yaki na mutumtaka da neman gaskiya da adalci da su kasance masu tsayawa a gefen dama na tarihi, tare da dukkanin abunda zasu iya, na ruhi da kuma kafofin watsa labarai, don taimakawa wadanda aka zalunta, da kuma aikin dakile sarautar alakakai ta Amurka da tsinanniyar 'yarta a yankin.
6. Majalisar Ahlul-baiti ta duniya, ta bukaci dukkan malamai, masana da kwararrun masu iya magana, da rubutu da alqalami da kafafen yada labarai a duk fadin duniya da su samar da fagen taimakon wadanda ake zalunta aka raba su da muhallansu a halin yanzu saboda yaki wajen bayyana gaskiya ta hanyar amfani da dukkan hanyoyin sadarwa zuwa Musamman a kafofin sadarwar zumunta ko ta hanyar gudanar da taruka da muzaharori, ayyukan yada labarai, da sauransu, suna sanar da al'ummar musulmi da 'yantattun al'ummar duniya, musamman ma matasa, game da halin da ake ciki yanzu na musubar da ɗan adam ke ciki.
7. Kum ga dukkan al'ummar musulmi, cibiyoyi da kungiyoyin Musulunci, da kasashen yankin, musamman Iran, Iraki, da Siriya, da kuma haramomi masu tsarki, wadanda suka karbi bakuncin 'yan gudun hijirar Labanon wadanda yakin ya rutsa da su tare da sadaukar da kansu da gidajensu wajen kula da lafiya, ilimi, da sauran hidimomi Majalisar Ahlul-baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) ta na mika godiya a bisa kokarinsu na bayyanawa da kuma biyan bukatar jagorancin kolin Shi'a koli na tallafawa wadannan mutane da ake zalunta tare da ci gaba da wadannan ayyuka na na ibada da mutuntaka.
A karshe, yayin da yake jinjinawa jagorancin babban sakataren majalisar duniya na Ahlul-Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, ga dukkan kokarin dukkanin bangarorinta cikin shekaru biyar da suka gabata, tare da fatan samun nasarar mjalissar cibiya mai tsarki a nan gaba da kuma girmama shahidan gwagwarmayar Musulunci a Gaza, Labanon, Iraki, Siriya da Yamen da kuma yi musu addu'ar samun daukaka a wajen Ubangiji Madaukakin Sarki, Yana mai mika godiyarsu ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma al'ummar Iran da Majalisar Ahlul-baiti ta duniya As, domin gudanar da wannan taro na majalisar koli.
و آخر دعوانا ان الحمد لله رب العالمین
Majalisar kolin duniya ta Ahlul-Baiti (As)
Qum mai tsarki
13 Rabi al-Thani 1446/26 Mehrmah 1403