
Bidiyon Yadda Aka Isra’ila Ta Kai Wa Asibitin Red Crescent Na Iran Da Ke Kan Iyakar Syria Da Lebanon Hari Da Makamai Masu Linzami 11
12 Oktoba 2024 - 05:10
News ID: 1493708
Afshar, Sakatare Janar na Kungiyar agaji ta Red Crescent a wurin asibitin filin Red Crescent a Siriya: A jiya ne mayakan gwamnatin yahudawan sahyoniya suka kai hari kan asibitin mai dauke gadajen kwantarwa 56 na kungiyar agaji ta Red Crescent na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da makamai masu linzami 11. Abin takaici, harin ya shafi tare da lalata rumbunan ajiyar kayayyaki, wurin ajiyar magunguna da wasu motocin daukar marasa lafiya.
