Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya kawo maku rahoto cewa: Biyo bayan shahadantar shugaban gwagwarmaya marikin tuta da neman 'yancin Quds da Palastinu, Hujjatul-Islam Wal Muslimin Sayyid Hasan Nasrallah da kuma tunawa da zagayowar ranar farko ta guguwar Al-Aqsa ta mayakan gwagwarmayar Musulunci na Palastinu, a yau Juma'a 3 ga watan Oktoba ne aka gudanar da sallar Juma'a a birnin Tehran karkashin jagorancin jagoran juyin juya halin Musulunci a Musalla na Imam Khumaini inda ya samu halartar dinbin al'umma kamar yadda zaku gani a wadannan hatunan dake ƙasa.














