Da yammaci ranar Talata 01/10/2024, wanda ya yi daidai da 28/03/1446, Shaikh Yakub Yahya Katsina ya jagoranci addu'ar Uku ta shahadar Sayyid Hasan Nasrullah, wanda Isra'ila ta shahadantar dashi a ranar Juma'a ta da gabata.
Kafin jawabin su Malam, an gabatar da saukar Alkur'ani mai girma, sannan aka sadaukar da ladar zuwa ga ruhin Shahid Hassan, tare da sauran waɗanda suka yi shahada a tare.
Cikin jawabin da Shaikh Yakub Yahya Katsina ya gabatar, ya kawo takaitaccen tarihin yadda aka assasa ita kanta kungiyar Hizbullah, tare da kalar sadaukarwa da dakarun ta suka yi wajen fitar da Isra'ila a yankin lokacin da suke kokarin mamayarta.
“Tun ranar da aka naɗa Sayyid Hasan Nasrullah, a matsayin shugaban kungiyar Hizbullah, yake sauraren shahada har zuwa ranar Juma'ar nan da ta gabata, tsawon shekaru arba'in kullum yana jiran shahada, shi a wajen shi wannan ba bakon abu bane, ba kuma sabon abu bane, ba bazata bane".
"Miyasa muka damu game da Shahadar shi? Saboda mun san shi, kuma mun san jajircewar shi, kuma mun san tsayuwar sa, kuma shi Malami ne, mai taƙawa, Malami ne da Allah ya bashi fikira ta iya isar da sako. Ba wata gwagwarmayar a wannan duniyar a yanzu, wadanda basu koyi wani abu ba a wajen Sayyid Hasan Nasrullah ba.
Daga karshe an gabatar da addu'a ta musamman zuwa ga tsarkakan ruhin shi, tare da sauran shaidan da suka yi shahada a tare.
لبيك_يارسول_الله
شهر_المولود_النبوي_الشريف
النبي_أولى_بالمؤمنين_من_أنفسهم
29_04_1446H.
02_Oct_2024M
Sheikh Yakub Yahya Katsina




















