27 Satumba 2024 - 16:11
Yadda Wakilan Kasashe Suka Fice Daga Zaman Taron Majalisar Dinkin Duniya A Daidai Lokacin Da Dan’Tadda Masha Jini Netanyahu Ya Fara Jawabi + Bidiyo Da Hotuna

Netanyahu: Ina da sako ga Iran, idan kun cutar da mu, za mu cutar da ku. Domin Idan har Hamas ba ta mika wuya ta sako fursunonin ba, to za a ci gaba da yaki. Kuma Isra'ila za ta yi duk mai yiwuwa don ganin cewa Iran ba ta samu makamin nukiliya ba.

Netanyahu ya fara jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya yayin da daywa daga wakilan suka fice daga dakin taron inda ganin hakan ya ce: Isra'ila ta na neman zaman lafiya da sulhu.

Ficewar wakilan kasashe da dama daga zauren taron, ciki har da kasashen da Netanyahu ke ikirarin aminanta da su, a daidai lokacin da ya fara jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Yayin da ya zamo kujeru babu kowa a yayin jawabin Netanyahu a zauren Majalisar Dinkin Duniya haka ya gudanar da jawabin na sa.

A jawabin da ya yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya, firaministan gwamnatin Sahayoniya ya yi ikirarin cewa wannan gwamnatin na neman zaman lafiya ne da sulhu. Amma Isra'ila na adawa da duk wani nau'i na mulkin Hamas a Gaza bayan yakin borin kunya.

A wani bangare na jawabin nasa Netanyahu ya ce: "Bayan ranar 7 ga watan Oktoba, Iran ta kaddamar da hare-hare a kan mu ta wasu bangarori 6.

 A yayin jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya, Netanyahu ya nuna hoton taswirar kasashen da ke gwagwarmaya bisa jagorancin Iran

Inda ya ce: na zo ne saboda kasata na fama da yaki, amma na yanke shawarar zuwa ne in amsa karyar da aka dangana mana. Domin muna fuskantar azzaluman makiya da suke son halaka mu.

Ba za mu hutawa ba har sai duk mutanen da aka sace akai garkuwa da su sun dawo. Wasu daga cikin iyalansu suna nan tare da mu, ina rokon su da su tashi tsaye.

Ina da sako ga Iran, idan kun cutar da mu, za mu cutar da ku. Domin Idan har Hamas ba ta mika wuya ta sako fursunonin ba, to za a ci gaba da yaki. Kuma Isra'ila za ta yi duk mai yiwuwa don ganin cewa Iran ba ta samu makamin nukiliya ba.

Netanyahu ya kara da cewa: Hezbollah ta harba mana rokoki sama da 8,000 tun ranar 8 ga Oktoba.