Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya bayar da rahoton cewa: masu
amfani da kafar sada zumunta ta X sun wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna
'yan sandan Jamus suna tsare da wani yaro dan shekara goma da ke rike da tutar
Falasdinu a hannunsa don yin Allah wadai da yakin da ake yi da Gaza.
