14 Satumba 2024 - 05:23
Amurka: Ministan Harkokin Wajen Afirka Ta Kudu Ya Yi Kira Da Goyi Bayan Falasdinu

Ronald Lamola yana mai tabbatar da cewa duk da 'banbancin ra'ayi' da ke tsakanin Amurka da Afirka ta kudu kan 'wasu batutuwa, dangantakar Afirka ta Kudu da Amurka tana da amfani ga juna.

A ziyarar da ya kai kasar Amurka, ministan harkokin wajen Afrika ta Kudu Ronald Lamola a ranar Juma'a ya yi kira ga duniya da su goyi bayan Falasdinu.

Lamola a taron Majalisar Dokokin Black Caucus na Majalisar Dinkin Duniya karo na 53 na shekara-shekara da akja gudanar a Washington D.C. ya ce: "Muna ci gaba da yin kira ga lamiri na gamayya na al'ummar duniya da su tsaya cikin numna goyon bayansu ga al'ummar Falasdinu ... don kiran Isra'ila da ta dakatar da kisan kiyashin da ke aukarwa a halin yanzu a Gaza”.

Kamar yadda ya fada "Za mu ci gaba da yin hakan, duk da barazanar da ke fitowa daga sassan duniya, saboda mun yi imanin muna tsaye kan ka'idoji,".

"Makomar duniya ta dogara ne da bin doka da oda daga dukkan al'ummomi, in ji Lamola, wanda ke ziyararsa ta farko zuwa Amurka bayan an nada shi a watan Yuli.

A ranar Alhamis din nan ne ya isa birnin Washington na tsawon mako guda, a dai dai lokacin da rahotanni ke cewa jami'an diflomasiyyar Isra'ila na neman 'yan majalisar dokokin Amurka su matsa wa Afirka ta Kudu lamba kan ta janye karar da ta ke yi na kisan kiyashi kan Tel Aviv a kotun duniya ta ICJ.

Jadawalin nasa a ziyarar da mai magana da yawunsa Chrispin Phiri ya fitar, bai nuna ko Lamola zai gana da takwaransa na Amurka ba.

Bayan nadin nasa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya buga waya ga Lamola domin taya shi murna.

Kasashen biyu sun tattauna kan yakin Rasha da Ukraine da kuma yakin Isra'ila a Gaza

Lamola ya shaida wa mahalarta taron a Washington, wadanda suka hada da ‘yan majalisar dokokin Amurka da kuma fitattun ‘yan kasashen waje na al’ummar Afirka cewa: "Muna ci gaba da kare hakkin bil'adama a Gaza. Muna tare da al’ummar Falasdin,”.

Ya ce: "Wannan wani matsayi ne mai cike da tarihi na gwamnatin Afirka ta Kudu" yayin da yake tunawa da kalaman jarumin yaki da wariyar launin fata Nelson Mandela, wanda ya ce: "Mun sani da kyau cewa 'yancinmu bai cika ba, ba tare da 'yancin Falasdinawa ba".

Martanin ‘Marar Dacewa’ Daga Isra'ila

"Duniya duka ta yi tsit" lokacin da Afirka ta Kudu ta dauki matakin kai karar Isra’ila zuwa kotun ICJ, in ji Lamola.

Da yake maida martini na harin da Hamas ta kai na bara, ya ce, "Martanin da kasar Isra'ila ta mayar kan lamarin na ranar 7 ga watan Oktoba bai dace da laifin da aka aikata ba".

Lamola Wanda ya hai matakin kwararren lauya alokacin daya wuce ya ce: “Abin ya wuce kare kai kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tsara kuma a kan haka ne muka garzaya kotun kasa da kasa domin neman a tsagaita bude wuta, domin a daina cin zarafin mata marasa laifi da yara, don dakatar da lalata Gaza”.

Kotun ta yi nuni da cewa Isra'ila "ya kamata ta daina ayyukan soji, don dakatar da lalata kayayyakin more rayuwa," Lamola, wanda ya taba rike mukamin ministan shari'a a wa'adin shugaba Cyril Ramaphosa da ya gabata, ya kara da cewa: "Duk da hukuncin kotun Isra'ila na ci gaba da yin hakan. .”

Da yake nuni da rikici a Ukraine, ya ce matsayin Afirka ta Kudu na rashin jituwa da ke faruwa ya kasance "mai samar da zaman lafiya da dimokiradiyya."

"Ba mu da shakka game da ikon mallaka da 'yancin kai na dukkan al'ummomi," in ji shi yana jaddada cewa "bai kamata a bar ayyukan da ba bisa ka'ida ba suna gudana."

Da yake tunatar da Arewacin Duniya game da illolin yake-yake, Lamola ya ce ‘yan Afirka sun cutuwa -abun yafi shafarsu- sakamakon tasirin alakoki masu daraja, gami da samar da abinci.

Dangantaka Mai Fa'ida Tare Da Amurka

Ba tare da nuna damuwa ba, Lamola ya tabbatar da "bambancin ra'ayi" da Amurka kan "wasu batutuwa".

Duk da haka, da yake ba da kyakkyawar sanarwa tare da yin kira na yin aiki "bisa hanyar tattaunawa mai ma'ana," ya ce dangantakar kasashen biyu "bai kamata ta dogara da barazana ba sai dai bisa mutunta juna".

"Mun yi imanin dangantakarmu da Amurka tana da moriyar juna kuma muna daraja wannan dangantakar," in ji shi.

Ya ce: Kuma Washington kuma tana amfana da wannan dangantakar wacce Dangantaka ce da dole ne a kiyaye ta".

"Bari mu shiga cikin bambance-bambance amma zamu iya yarda da wani sabanin," in ji shi, yayin da yake jawabi ga gwamnatin Joe Biden.

Ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu "Ba za mu gaya wa Amurka abin da ya kamata ta yi ba’ kuma muna fatan Amurka ba za ta gaya mana abin da yakamata mu yi ba".

Ya kara da cewa: "Za mu ci gaba da kasancewa a fayyace don gamsarwa da kuma fatan za mu iya shawo kan Amurka kan batutuwa da dama a bangarori daban-daban kuma hakan ya zama dangantakar mutunta juna".