6 Satumba 2024 - 18:56
Chadi: Ruwan Sama Da Guguwa Sun Kashe Mutane 15 A Chadi

Jami'an kasar Chadi sun bayyana cewa ruwan sama da iska mai karfi a gabashin kasar ya kashe dalibai 14 da daya daga cikin malamansu.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahoto bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na IRNA bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar AFP cewa, jami’an wannan kasa ta Afirka sun sanar da cewa an ci gaba da samun ruwan sama da guguwa mai tsanani a wannan kasa a ranakun Laraba da Alhamis, lamarin da ya yi sanadin rugujewar rufin ajujuwa tare da mutuwar mutane 15.

A sa'i daya kuma, ofishin firaministan kasar Chadi ya bayyana cewa: "Tsawa ta fadawa makarantar, inda ta kashe mutane 15 tare da jikkata wasu da dama".

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar Chadi a watan da ya gabata ya kashe mutane akalla 54. A halin da ake ciki kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Talata game da tasirin "damina da ruwan sama mai karfi" a kasashen Afirka ta Tsakiya, ta kuma kara da cewa: kasar Chadi ce kasar da ta fi fama da bala'in kuma kimanin mutane 247,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a 'yan makonnin nan.

A halin da ake ciki, ruwan sama da ambaliyar ruwa a Nijar da ke makwabtaka da kasar Chadi sun kashe mutane 273 tare da lalata rayuwar mutane sama da 700,000 tun daga watan Yuni.

A ko da yaushe masana kimiyya suna yin gargadin cewa sauyin yanayi da gurbataccen man fetur ke haifarwa ya kara tabarbarewar yanayin tare da haifar da ambaliya akai-akai.