Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta
maku cewa: Tashar yada labarai ta Kan Isra’ila ya bayar da rahoton cewa,
sama da malaman addinin yahudawan Amurka 100 ne suka rubuta wasika ga Benjamin
Netanyahu, inda suka bukaci ya amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da
kuma musayar fursunoni.
A cewar sanarwar cibiyar sadarwa ta "Kan", wannan wasiƙar ta ce: "Karbar yarjejeniya abu ne da ya shafi Yahudawa da ɗabi'a wanda ya kamata a gudanar da shi yanzu".