19 Yuli 2024 - 19:29
Yadda Aka Muzahara Ranar Ashura A Jihar Michigan Ta Amurka + Bidiyo

Yadda Makokin Al’iummar jihar Michigan ta Amurka ya gudana tare da daga tutar Falasdinu Muzahara ranar Ashura a jihar Michigan ta Amurka tare da amsa kran Labbaika Ya Husain, Labbaika Ya Khamenei tara da tunawa da shahidan Karbala da na Gaza. Idan bamu a Gaza, a kalla ya kamata mu zama muryarsu ga al'ummar duniya, mu yada a kafofin yada labara irin zaluncin da akewa al'ummar Palastinu. Kamar kowace shekara, an gudanar da tarukan Tasu'a da Ashurar Imam Husaini tare da hadin guiwar kungiyoyin makoki a birnin "Dearborn" dake jihar Michigan ta kasar Amurka. Masu zaman makoki - wadanda kasantuwar mafi yawansu samari ne ya burge sosai - sun sabunta alkawarinsu da Sayyidushl-Shuhada (a.s) da sunnonin Ashurai da anbaton "Labbaik Ya Husain". Wani abin ban sha'awa sosai a taron makoki na jihar Michigan a wannan shekara shi ne daga tutar Falasdinu don nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da kuma tutoci na yin Allah wadai da laifuffukan gwamnatin sahyoniyawan da ke kashe kananan yara. Har ila yau, sun daga zane-zane da hotuna a hannunsu wadanda suka kwatanta laifin ta’addanci da Yazid ya aikata a shekara ta 61 bayan hijira da kuma laifukan da Isra'ila take aikata a duniya a yau ga mutanen Gaza da Falasdinu. Masu makoki na Husain a Michigan sun kuma yi kira ga Musulmi da masu ‘yanci na duniya da su kaurace wa kayayyakin Isra’ila.