Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Kafofin
yada labaran Amurka sun bayar da rahoton wani yunkurin kashe Donald Trump a
lokacin da yake jawabi a wurin gangamin zabensa a jihar Pennsylvania ta Amurka.
A cewar wadannan kafafen yada labarai na Amurka, wani mutum ya harbi Trump, amma harsashin ya doki kunnen sa na dama kuma jini ya kwarara daga jikin kunnen.
CNN ta ruwaito cewa jami'an hukumar leken asiri ta Amurka sun yi gaggawar cire Donald Trump daga dandalin bayan da ya fadi kasa a wani gangami da aka yi a jihar Pennsylvania. Inda jami'an suka taimaka masa har ya iya tsayawa, fuskarsa ta yi ta zubar da jini.
A cewar wannan rahoto, yana ta ihun jama’a yana daga hannu, daga nan ne jami’an suka dauke shi zuwa wata mota suka bar wurin.
"lafiyar Trump na da kyau kuma a halin yanzu ana duba lafiyarsa a wata cibiyar kula da lafiya," in ji kakakin Trump Steven Chong.
Ma'aikatar leken asirin Amurka ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi game da harbe-harben kuma za a fitar da karin bayani idan aka samu.
Cibiyar sadarwar boye ta CNN bisa nakaltowa daga majiyoyin jami’an tsaro a Amurka, ya tabbatar da cewa an kashe wanda ya yi harbin a wajen gangamin zaben tsohon shugaban kasar nan, Donald Trump a jihar Pennsylvania.
Gidan yanar gizon CNN Ya kuma ambato lauyan gundumar Butler Richard Goldfinger na cewa an kashe daya daga cikin wadanda suka halarci gangamin da dan bindigar.
Ya kara da cewa yanayin wani da ya halarci wannan taro yana da matukar muni wanda shima abu ya shafa.
Martanonin da akai ga yunkurin kisan Trump
Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa dan Donald Trump ya bayyana lamarin a matsayin "ta'addanci" a dandalin sada zumuntarsa na X.
Dangane da kisan Trump da bai yi nasara ba, wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi hasashen cewa watakila shi ne ya shirya yukurin kisan na sa kuma wani shiri ne na neman karin kuri'u.
Gwamnan Pennsylvania ya ce: "Ba za’a taba yarda da cin zarafi ga kowace jam'iyya da shugaban siyasa ba."
Sanata Chuck Schumer, shugaban mafi rinjayen jam'iyyar Democrat a majalisar dattawan Amurka, ya ce bayan yunkurin kisan gillar da aka yi wa Donald Trump: "Na firgita da harbin da aka yi a wurin taron zaben Trump, amma yanzu na ji sauki".
Da yake mayar da martani game da harbin da aka yi wa Donald Trump, kakakin majalisar dokokin Amurka Mike Johnson ya ce: "Wannan mummunan aiki na tashe-tashen hankula na siyasa a wani gangamin zanga-zangar lumana ba shi da wani matsayi a kasar, kuma dole ne a yi Allah wadai da shi baki daya".
Dangane da yunkurin kisan da aka yi wa Donald Trump da bai yi nasara ba, Barack Obama ya rubuta a shafin labarai na X cewa: Ko da yake har yanzu ba mu san ainihin abin da ya faru ba, amma ya kamata mu yi farin ciki yanzu da ba a yi wa Trump mummunar illa ba.
Ya kamata a lura da cewa yunkurin tashin hankalin da makami a Amurka lamari ne na damuwa da wanda yawan makamai a kasar ya fi yawan al'ummarta.
Cibiyar "yaki da muggan Makamai" ya yi rikodin mutuwa sama da 40,000 ta dalilin harbin bindigogi a bara. Kokarin takaita makamai a kasar nan a kodayaushe na fuskantar adawa daga ’yan siyasa da masu fafutukar neman makamai.
