4 Yuni 2024 - 14:46
ABNA Ya Yi Tattaunawa Ta Musamman Tare Da Sheikh Ibrahim Zakzaky/ Tasirin Mazhabar Khumaini (RA) A Kan Matasan Najeriya / Imam Khumaini (RA) Ya Kasance Hakikanin Alamar Musulunci + Bidiyo

Babban shugaban Harkar Musulunci a Najeriya: Mun koyi hanyar yin wa'azinmu daga Imam Khumaini (RA) ne, Imam Rahal bai ce ku zo ku bi wata mazahaba ba, sai dai ya aksance yana cewa mu dukanmu Musulmi ne, ku ya zama wajibi mu yi wa Musulunci aiki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) na kasa da kasa – Abna: A ranar 5 ga Mayu, 1953 (15 ga Urdubihisht 1332) a birnin Zariya da ke arewacin Najeriya an haifi yaro mai albarka mai suna Ibrahim, kuma bayan shekaru, tare da yin koyi da tafarkin Khumaini Kabir, ya zama mutum mai tasiri a duniyar Musulunci. An haifi Ibrahim a gidan Ahlus Sunna mabiya mazhabar Malikiyya. Da ya ke yawancin Musulmin Afirka ta Yamma Malikiyya ne. “Ibrahim Zakzaky” ya shagalta da koyon iimin addini hadi da yin karatun zamani. Don haka ya je birnin Kano (arewacin Najeriya) inda ya yi karatu a makarantar koyon larabci.

A shekarar 1975 (1354) ya shiga Jami’ar Ahmad Bello da ke Zariya, bayan ‘yan shekaru kuma ya sami digiri na farko a fannin tattalin arziki a wannan jami’a. Saboda dimbin ayyukan ilimi da tarbiya da ya yi a jami'a, ya zama memba na kungiyar dalibai musulmi bayan wani dan kankanin lokaci sannan ya zama babban sakataren wannan kungiya.

Tafiyarsa Zuwa Faransa Da Ganawarsa Da Imam Khumaini (RA)

A lokacin da yunkurin Imam Khumaini (RA) ya fara yaduwa da kuma fadada shuhura ta jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Shekh Zakzaky ya kasance yana da sha'awar bibiyar wadannan labarai da ci gaba da wannan yunkuri na Imam. Soyayyar Sheikh Ibrahim ke yiwa Imam ta kai shi ga ziyarar Imam (RA) a birnin Paris. Ganawar da ta kasance ta ayyana makoma ga Shekh Ibrahim da miliyoyin wasu 'yan Najeriya.

Tafiyarsa Zuwa Iran Da Ganawarsa Da Imam (RA) A Iran

A farkon juyin juya halin Musulunci na Iran, Ibrahim Zakzaky a matsayinsa na mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kasa da kasa na kungiyar Daliban Musulmi ta Najeriya ya yi tattaki zuwa Iran tare da wasu gungun dalibai inda suka je ganin Imam (RA). A wannan ziyarar Imam ya ba shi kyautar Alqur'ani ya ce: Ka je ka shiryar da al'ummar kasarka da Alkur'ani. Wannan umarni na Imam Khumaini (RA) ya wadatar da shi shiga makarantar hauza ta Kum don koyon ilimin addini.

A yanzu shi ne “Sheikh Ibrahim Zakzaky” wanda baya ga cikar saninsa da fikihun Sunna da Shi’a, ya zamo shi ne ma’abucin isar da sakon Ahlul Baiti (a.s) da kuma juyin juya halin Musulunci na Iran ga al’ummar Nijeriya.

Farkon Harkar Musulunci A Nijeriya

Tare da fara ayyukan Sheikh Ibrahim da tasirin da'awarsa ta addinin musulunci ga rayuka masu shaukin hakan a sassa daban-daban na Najeriya, To an fara damuwowi kan wannan guguwar mai fadi da ta ke ta yadu kamar wutar daji. Gwamnatin Najeriya karkashin tasirin Turawan Yamma, yahudawan sahyoniya da Wahabiyawa, ta haramta ayyukansa na addini tare da daure Zakzaky tsawon shekaru 9 a gidan yari bisa zargin haifar da fitina da kuma tada zaune tsaye atsrain rayuwa na yau da kullum na jama’a.

Fadadar Ayyukan Anfanuwa Ga Zamantakewa Da Kuma Yadda Ake Ta Shiga Makarantar Ahlul-Baiti A Najeriya

Samar da makarantun Islamiyya kusan 300 a Najeriya da makwaftan kasashe, da kafa cibiyoyin kula da marayu da samar da cibiya da nufin samar da aikin likitanci da na raya kasa da na ilimi ya sanya soyayyar Sheikh Ibrahim a cukatan ‘yan Najeriya.

Yada addinin mai rinjaye na musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (a.s) wanda aka fara shi da wasu tsirarun mutane, yanzu ya kai matsayin da kusan mutane miliyan 12 a Najeriya suna bin mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ne. Najeriya na daya daga cikin kasashen da mabiya Shi'a suka fi yawa a duniya....

Za Mu Ci Gaba