4 Satumba 2022 - 19:58
Dan Wasan Karate Na kasar Kuwait ya Janye Daga Gasar League don karawa Da Dan wasan Isra’ila

Rahotanni sun bayyana cewa Dan wasan Karate na kasar Kuwait Mohammad Al-Otaibi ya janye daga wasan karate na piremire legue na daya da ake bugawa a birnin Baku na kasar Azarbaijan don kada ya kara da Abokin hamayyarsa na Isra’ila saboda nuna goyon bayansa ga Alummar falasdinu da isra’ila ke jagoranta, da kuma nuna adawa da mayar da hulda da israila.

Tun da fari an tsara cewa dan wasan kasar Kuwait zai kara da abokin hamayyarsa na Isra’ila a ajin nauyi na kilograme 60 sai dai ya sanar da janyewa daga gasar don kar ya kara da abokin karawarsa da dan Isra’ila mai suna Ronen Gehtbarg

Wannan ci gaban yana zuwa ne bayan da yan wasa musulmi daga kasashen duniya ke kin karawa da yan wasan Isra’ila a wasanni na kasa da kasa, domin nuna rashin amincewa da ci gaba da zaluntar falasdinawa da Isra’ila ke yi da kuma ci gaba da mamaye yankunasu da take yi.

Da dama na ganin shigar yan wasan isra’ila a wasannin motsa jiki a matsayin wani shiri na taimakawa Isra’il ta sanya hannu kan yarjejeniya daidaita dangantakarta da kasashen musulmi da na larabawa duk da irin zalunci da laifukan da take tafkawa kan alummar falasdinu

342/