15 Faburairu 2022 - 09:35
Iran : Ana Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Iman Ali (a.s)

A Iran, an kwashe daren jiya ana bukukuwan murnar zagayowar ranar haihuwar Iman Ali (a.s)

An haifi Imam Ali, wanda shi ne mutum na farko da ya musulunta, sannan kuma surukin Manzon Allah mai girma, Muhammad ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da zuriyarsa), a ranar 13 ga watan Rajab (wata na bakwai na kalandar musulmi) kimanin shekara ta 600 a dakin Ka'aba da ke birnin Makka.

Haka nan Imam Ali (a.s) ya yi hidima wajen yada addinin Musulunci a duniya kuma ya shahara da juriya da kunya da jajircewa da kishin musulinci.

A Iran, mutane sun yi wa masallatai da gidaje da tituna da kantuna ado da kayan ado da fitulu masu launi tare da rarraba kayan zaki da alewa a matsayin wata hanya ta murnar zagayowar ranar haihuwar Imaminsu na farko.

Haka kuma ranar a Iran akan yi mata takan ranar mahaifi ko ta mazaje.