Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Muhammad Al-Bukhaiti shugaban bangaren siyasa na kungiyar yana fadawa tashar talabijin ta Al-Alam ta Larabci da ke watsa shirye-shiryenta a nan birnin Tehran a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa babu makawa za mu maida martani kan makiyammu har sai sun mika wuya ga bukatummu na samun ‘yenci da kuma barimmu mu rayu a matsayin ‘yentacciyar kasa.
Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne kasar saudia da kawayenta suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar da karfi.
Amma yau shekaru 7 ke nan sun kasa yin haka sun kuma kasa samun nasara a kan sojojin Yemen da kawayensu na sojojin sa kai a cikin gida. A nan ne suka dawo kan hare-hare ta sama kadai inda suke kashe fararen hula suke kuma lalalata duk wani abu mai kyau da ya rage a kasa.
342/