Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hatem al-Assi, kwamandan dakarun Larabawa a Kirkuk, ya yaba da sadaukarwar da Janar Qassem Soleimani da Abu Mahdi al-Mohandes, jagororin gwagwarmaya suka yi, ya kuma jaddada cewa idan da ba mu sadaukar da wadannan kwamandojin shahidan ba, yankunanmu za su ci gaba da kasancewa karkashin mamayar ISIL.
“A jajibirin zagayowar ranar shahadar kwamandojin gwagwarmaya, muna tunawa da yadda shugabannin da suka yi nasara suka taka rawa wajen kwato yankunanmu na Hawija, al-Rashad da Riyadh daga hannun kungiyoyin ta’addanci na ISIL tare da kula da ‘yan gudun hijira a yankin da ake yaki, ta hanayar ayyukan jin kai," in ji al-Assi a cikin wata sanarwa.
Ya ce ko shakka babu wadannan manyan kwamandoji sun bayar da babbar gudunmawa wajen kubutar da Iraki daga fadawa hannun 'yan ta'addan daesh.
Kamar yadda kuma su ne suka kafa dakarun sa kai na Hshd Alshaabi, wadanda har yanzu su ne gishikin zaman lafya a Iraki da kuam hana 'yan ta'adda sakata fadin kasar.
342/