28 Disamba 2021 - 17:18
An Dakatar Da Fira Ministan Sumaliya Saboda Zargin Cin Hanci Da Rashawa

Shugaban kasar Sumaliya Mohammad Abdullahi Mohammad da aka fi sani da suna Farmajo ya sanar da dakatar da Fira Ministan kasar daga mukaminsa bayan da aka zarge shi da cin hanci da rashi da almundahana da kudaden Baitul mali, kana kuma ya umarci dakarun tsaron kasar da su koma karkashin umarninsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan matakin yana zuwa ne bayan da aka samu hatsaniya tsakanin manyan shuwagabanin guda biyu, game da batun shirye- shiryen da ake yi na gudanar da zabuka a kasar, tuni hukumomi masu fada aji na duniya suka bukaci ofishin jakadancin Amurka a Magadishu da tsoma baki wajen an shawo kan matsalar kada ta watsu a wasu sassan kasar,

Har ila yau ya fadi cewa “ina sanarwa da Al’ummar kasar Sumliya cewa gwamnatin kasar ta sauke nauyin da ya ratawa a wuyanta musamman a lokacin mulkin rikon kwarya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, don haka na Umarci dukkan jami’an tsaron kasar da su koma karbar umarni daga offishin fira ministan kasar, kuma an sanar da sunan Mohammad Hussain Roble a matsayin sabon fira ministan riko na kasar.

Yanzu haka dai kungiyoyi masu Jihadi a kasar kamar su Al-shabab ne ke iko da bangaren mai yawa na kasar, kuma suna kai hare hare a babban birnin kasar.

342/