24 Disamba 2021 - 18:38
Daruruwan Al'ummar Moroko Ne Suka Yi Zanga-zangar Adawar Da Kulla Hulda Da Isra’ila

Daruruwan Mutane daga ko ina a fadin kasar Moroko ne suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da cika shekara 1 da kasar ta sake kulla hulda da HKI ,tare kuma da nuna goyon bayansu alummar falasdinu da ake zalunta,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Zanga-zangar ta samu halartar jami’iyun siyasa da kungiyoyin kare hakkin bil adama guda 15 da suka nuna goyon bayansu ga Alummar faladinu da kuma yin tir da sake kulla hulda da gwamnatin kasar ta yi da HKI.

Masu zanga-zangar sun rika rera taken yin Allah wadai da kulla hulda da Ira’aila da kuma bukatar a soke duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin kasar da gwamnatin yahudawan sahyuniya, da suka bayyanshi a matsayin abin kunya.

Sai dai jami’an tsaron sun yi yunkurin tarwatsa masu zanga zangar musamman a Biranen Casabalanca da kuma Rabat fadar mulkin kasar.a shekara ta 2020 ne Moroko ta kulla hulda da HKI. Da taimakon Amurka.

342/