Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta bayyana cewa jiragen na saudiya da kawayenta sun kai hare-haren en a kan wuraren da babu kayakin soje ko sojoji a wajnesu. Banda haka labarin ya kara da cewa a jiya Jumma’a ma jiragen yakin na Saudiya sun kai hare-hare kan birnin na San’aa.
Labarin ya kara da cewa Saudiya da kawayenta suna kai irin wadannan hare-hare ne a daidai lokacinda mayakan na gwamnatin da na sa kai suke samun nasara a kan sojojinmsu a kasar a lardin Ma’arib na kudancin kasar.
Tun shekara ta 2015 ne gwamnatin Saudiya ta farwa kasar da Yaki da nufin maisa tsohon shugaban kasar Abdurabbu Mansr Hadi kan kujerar shugabancin kasar. Yakin da kashe dubban mutane miliyoyi suna cikin yunwa sannan wasu miliyoyin sun zama ya gudun hijira a ciki ko a wajen kasar.
342/