5 Nuwamba 2021 - 17:55
Kungiyar AU Ta Damu Da Halin Da Ake Ciki A Habasha

Kungiyar tarayyar Afrika, ta nuna matukar damuwa game da halin da ake ciki a kasar Habasha.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shugaban hukumar ta (AU) Musa Faki Mahamat, ya bayyana matukar damuwa dangane da ta’azzarar ayyukan soji a kasra ta Habasha.

Wata sanarwa da AU ta fitar, ta ruwaito shugaban na kira da a tsagaita bude wuta, sannan a girmama rayuka da dukiyoyin fararen hula tare da kayayyakin gwamnati.

Haka kuma ya bukaci bangarorin dake rikici su hau teburin sulhu domin lalubo hanyoyin warware matsalolinsu domin ci gaban kasar.

Har ila yau, Moussa Faki Mahamat ya bukaci bangarorin su kiyaye cikakken ’yanci da yankunan kasar da hadin kan al’ummarta.

Ya kara kira ga bangarorin su gargadi magoya bayansu game da kalaman kiyayya da ingiza rikici da rarrabuwar kawuna.

Ya kuma jaddada cewa, AU na nan kan bakanta na ci gaba da hada hannu da dukkan bangarorin domin cimma matsayar siyasa guda.

Halin da ake ciki a Habasha, ya dau hankalin duniya ne bayan da ‘yan tawayen TPLF, suka yunkuri tunkarar Adis Ababa babban birnin kasar, a daidai lokacin da gwamnatin Aby Ahmed, ta ayyana dokar ta baci a duk fadin kasar.

342/