Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ana sa bangaren ministan wutar lantarki na kasar Siriya Ghassan Al-zamel ya bayana cewa harin da aka ki kan bututun ya haifar da koma baya da katsewar wutar lantarki a cibiyar raba wutar lantarki ta Dair Ali na dan wani lokaci, da kuma wasu yankuna a birnin Damaskas.
Minsitan mai na kasar Siriya ya sanar cewa tuni tashohin suka ci gaba da aiki bayan da aka gyarasu sakamakon harin da aka kai akan bututun iskar gas din,
Tuni dai aka fatattaki yan kungiyar ta Daesh daga yankunan kasar Siriya da Iraki, amma dai har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan kasashen biyu daga nesa.
342/