6 Satumba 2021 - 13:50
​Libya: An Saki Sa’adi Gazzafi, Dan Tsohon Shugaban Kasa Mu’ammar Kazzafi

Gwamnatin rikon kwarya da kuma hadin kan kasar Libya ta bada sanarwan sakin Sa’ad Kazzafi dan tsohon shugaban kasar Mu’ammar Kazzafi wanda aka kashe a shekara ta 2011 bayan an yi masa juyin mulki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Da farko dai sa’ad Kaizzafi ya arce zuwa kasar Niger bayan an yi wa mahaifinsa juyin mulki, amma daga baya aka dawo da shi gida Libya aka tsare shi a shekara ta 2014.

Labarin ya kara da cewa tuni Sa’ad Kazzafi ya tafi kasar Turkiyya. Har’ila yau wasu majiyoyin gwamnatin kasar Libya sun nakalto ma’aikatar shari’ar kasar na cewa Sa’ad kazzafi bai aikata wani laifi ba, shi ya sa aka sake shi.

342/