Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Ministan harkokin wajen Japan Toshimitsu Motegi ya shaida wa gidan talabijin na kasar ranar Lahadi cewa, wakilan kasashen Rasha da China su ma za su halarci taron.
Ministan harkokin wajen Japan din ya kara jaddada mahimmancin da wakilan kasashen Rasha da China ke da shi a wannan taro, yana cewa kasashen biyu suna da karfin fada a ji a Afghanistan.
Yace jakadojin kasashe kimanin 20 ne za su halarci wannan taro da zai gudana ta intanet, karkashin shugabancin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon gwamnatin da kungiyar Taliban za ta kafa nan gaba.
Kanuwan manyan kasashen duniya dai ya rabu, game da Afghanistan tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace mulki daga hannun gwamnatin Kabul.
Yayin da Amurka da kasashen turai suke ce basu shirya amincewa da gwamnatin da kungiyar Taliban zata kafawa ba, Rasha da China sun ce zasu zura ido har sai ga salon mulkin kungiyar ta Taliban.
342/