Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Sayyid Ra’isi ya bayyana cewa ana tattaunawa ne idan babu takurawa, amma idan an shiga tattaunawa tare da takurawa, wannan shi ne tursasawa, wanda Iran ba za ta taba amincewa ba.
Shugaban ya kammala da cewa tattaunawa domin farfado da yarjejeniyar JCPOA yana daga cikin ajendar gwamnatinsa, amma ba karkashin tursasawar kasashen Turai da Amurka ba.
Hatta turawa da kuma Amurkawa sun tabbatar da cewa ba za su iya tursasawa Iran shiga tattaunawa ba, sannan ba za ta shiga tattaunawa don kawai a tattauna, ba tare da fatan za’a sami sakamako mai kyau a hannu ba.
Daga karshe shugaban ya ce duk wata tattauna wacce ba za ta kaimu ga daukewa kasar Iran dukkanin takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar ba, ba za mu bata lokacimmu a irin wannan tattaunawar ba.
342/