26 Yuli 2021 - 16:49
Lauyoyin Sheikh Abduljabbar Sun Zargi Gwamnan Kano Da Katsalandan Cikin Shari’a

Lauyoyi masu kare fitaccen malamin nan na jihar Kano da ke arewacin Nijeriya Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, sun zargi gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da tsoma baki da kuma yin katsalandan cikin shari’ar da ake yi wa wanda suke wakilta, suna masu kiran gwamnan da ya bari shari’a ta yi aikinta.

ABNA24 : Lauyoyin ƙarƙashin jagorancin shugabansu Barrister Saleh M. Bakaro sun bayyana hakan ne a wata ganawa da suka yi da manema labarai a jiya Lahadi don fayyace matsayarsu kan abin da ke gudana a halin yanzu na shari’ar da ake yi wa Shehin malamin.

Barrister Bakaro ya shaida wa manema labaran cewa: Babban dalilin da ya sanya su nemansu a jiya Lahadin shi ne kan irin maganganu ‘masu tada hankali’ da gwamnan jihar Kano dangane da shari’ar da ke gudana wanda hakan wani riga malam masallaci ne kana kuma barazana da karen tsaye ga tafarkin shari’ar da ake yi wa wanda suke karewa, wato Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Malam Bakaro yayi zargin cewa gwamna Gandujen ya kwatanta wanda suke karewa ɗin da ƙungiyoyin nan biyu masu tada hankali da ta’addanci na Maitsatsine da Boko Haram wanda ya ce ko da wasa hakan bai dace ba ya fito daga bakin gwamnan a matsayinsa na gwamna kana kuma shugaban harkokin tsaro na jihar.

Har ila yau Barrister Bakaro ya ce gwamnan da kansa ya ce shi ya ba da umurnin a tsare Sheikh Abduljabbar da gidan yari na Kano, wanda ya ce a shari’a ba shi da ƙarfin da zai yi hakan, wannan aiki ne na kotu, wanda hakan yana nuni da irin yadda Gwamna Gandujen yake katsalandan da harkokin shari’a wanda ya ke jin tsoron ci gaban hakan zai yi shafar tafarkin shari’ar da ake yi wa wanda suke karewa.

Don haka ya kirayi gwamnan da ya guje wa yin hakan sannan kuma ya kirayi ‘yan jarida da ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya da kuma ƙungiyoyin fararen hula da su sanya ido sosai kan yadda ake gudanar da shari’a wa wanda suke wakilta.

A ranar Juma’ar can da ta gabata ce wato 16 ga watan Yuli jami’an tsaro suka kama Shehin malamin da kuma gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin zagi da cin zarafin Annabi (s.a.w.a) zargin da Shehin malamin ya musanta. Ana ci gaba da tsare malamin dai har sai zuwa ranar 28 ga watan Yulin inda kotu za ta ci gaba da sauraren ƙara.

342/