5 Yuli 2021 - 13:15
Gwamnatin Tigray Ta Buƙaci Janyewar Sojoji Kafin Tattaunawar Tsagaita Wuta

Gwamnatin yankin Tigray na ƙasar Habasha ta buƙaci cikakkiyar janyewar sojoji daga Eritea da kuma jihar Amhara da ke maƙwabtaka da yankin na su kafin ta shiga tattauanwar sulhu da gwamnatin tarayyar ta Habasha.

ABNA24 : A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin Tigray People's Liberation Front (TPLF) mai riƙe da yankin, Getachew Reda ya fitar a yau Lahadi ya ce za su amince da batun tsadaita wuta ne kawai idan har aka ba su lamunin cewa ba za a sake mamaye musu yankin su ba.

Har ila yau kakakin ya ce wajibi ne sojojin mamaya daga Amhara da kuma Eritrea su fice daga yankin Tigray sannan su koma inda suke a da kafin yaƙin da ya faru.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ce dakarun jam’iyyar TPLF mai mulkin yankin na Tigray kafin dakarun Habashan su kore su kore su daga wajen a watannin baya, suka dawo da kuma ƙwace ikon babban birnin yankin wato Mekelle.

Dawowar ta su ce ta sanya firayi ministan Habashan Abiy Ahmad sanar da tsagaita wuta ta ɓangare guda lamarin da TPLF ɗin ta bakin kakakin na ta Getachew Reda ta yi watsi da shi da kuma bayyana hakan a matsayin wasan yara.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga wajen gwamnatin Habashan kan wannan matsaya da jami’an yankin Tigray ɗin suka sanar.

Yaƙin da ya gudana tsakanin ɓangarori biyun dai yayi sanadiyyar mutuwar wasu dubban mutane da kuma tarwatsa wasu miliyoyi daga yankin.

342/