14 Yuni 2021 - 09:37
China : Yanzu Lokaci Ya Wuce Da Wani Karamin Gungu Zai Dinga Mulkin Duniya

Kasar China ta mayar wa da gungun kasashen G7, na kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya martani da cewa yanzu fa lokaci ya wuce da wani karamin gungu zai dinga mulkin duniya.

ABNA24 : Wannan dai na zuwa ne bayan da shugabannin kasashen gungun na G7 suka amince da wani shirin nuna adawa ga shirin kasar China da ke taimakawa kasashe matalauta wajen inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa.

Kasashen dai na ci gaba da sukar shirin kasar China da take dorawa kananan kasashe dimbin basuka, yayin da suke ganin zai yi wuya kasashen da ke amfana da kasar su iya sauke basussukan da ake bin su.

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta G7 dai, sun sha alwashin hada karfi da karfe don samar da daruruwan biliyoyin kayayyakin more rayuwa ga kasashe masu karamin karfi da masu matsakaitan kudaden shiga.

Saidai a cewar jakadan China a Landan, a wata hira da kamfanin dilancin labaren Reuters, kasashe ne baki dayansu ya kamata su zamna su tattauna makomar al’amuran duniya ta hanyar tuntuba.

342/