29 Maris 2021 - 19:55
An Kai Harin Kunar Bakin Wake Akan Wata Majami’a A Kasar Indonesia

Majiyar ‘ yan sandan kasar Indonesia ta sanar da cewa; Da safiyar yau Lahadi ne wasu mahara biyu ‘yan kunar bakin wake su ka kai hari akan majami’ar Roman Katolika da garin Makassar, wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutane 14.

ABNA24 : Majiyar ‘yan sandan kasar ta Indonisea ta ci gaba da cewa; An kai harin ne adaidai lokacin da mabiya darikar Roman Katolika da suke cikin majami’ar suke gudanar da ibadunsu.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin. Sai dai a shekarun baya an rika samun irin wadannan hare-haren da masu wuce gona da iri na addini suke kai wa akan majami’u.

Minstan harkokin addini na kasar ta Indenesia Yaqut Cholil Qoumas ya yi tir da harin, yana mai yin kira ga ‘yan sandan da su kara daukar matakai masu tsauri na bayar da kariya akan wuraren ibada.

342/