ABNA24 : A wani rahoto da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta fitar ta nuna damuwarta ainun kan irin ci gaba da hare-haren da ‘yan ƙungiyar nan ta Allied Democratic Forces (ADF) – ƙungiyar da asalinta daga ƙasar Uganda ta ke amma tana gudanar da ayyukanta da Demokraɗiyyar Kongon tun shekara ta 1995 – suke ci gaba da kai wa a ƙasar.
Kakakin hukumar ta UNHCR Babar Baloch ya ce tun daga farkon shekarar nan ta 2021, dakarun ADF ɗin sun kashe kimanin mutane 200, sun raunana wani adadi mai yawa da kuma tarwatsa wasu kimanin 40,000 daga muhallinsu a yankin Beni da ke Lardin Kivu ta arewa da ke Demokraɗiyyar Kongon.
Kakakin hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ci gaba da cewa: Кasa da watanni uku, an yi zargin cewa ‘yan ƙungiyar ta ADF sun kai hari ƙauyuka 25, inda suka sanya wuta kan wani adadi mai yawa na gidaje da kuma sace sama da mutane 17.
An jima dai ana zargin ƙungiyar ta ADF wacce ake zargin tana da alaƙa da ƙungiyar ta’addancin nan ta DAESH ko kuma ISIS da aikata irin waɗannan kisan gilla a ƙasar Demokraɗiyyar Kongon.
342/