ABNA24 : A cikin jawabin nasa, Donald Trump ya bayyana abin da ya faru na kaddamar da farmaki a kan babban ginin majalisar dokoki da cewa ba abu ne da ya dace da Amurka, inda ya ce dole ne mutane su zama masu kiyaye doka, amma ba tare da yi ishara da cewa magoya bayansa ne suka aikata hakan ba, kamar yadda kuma bai ishara da kalaman da ya yin a tunzura wadanda suka yi hakan ba.
Baya ga haka kuma Trump ya bayyana kansa a matsayin shugaban Amurka da ya yi nasara a cikin shekaru hudu wajen dawowa Amurka da martabarta a duniya, tare da hada kan kawayenta wajen tunkarar barazanar China a kan siyasar Amurka da tattalin arzikinta.
Ya ce babbar matsalar da ta auku a yanzu ita ce babu aminci da juna a tsakanin Amurkawa, kuma wanann shi ne abin da ya kamata a samu, domin Amurka ta zama abin koyi ga duniya.
Dangane da sabuwar gwamnati da za ta karbi ragamar iko a yau a kasar ta Amurka kuwa, Trump ya ce yana yi mata fatan samun nasara.
Trump dai yaki amincewa da cewa ya sha kayi a zaben shugaban kasa, duk kuwa da cewa bayan tunzura magoya bayansa da ya yi suka kaddamar da farmaki kan majalisar dokokin kasar a Washington, ya bayyana cewa ya amince zai bayar da hadin kai domin mika mulki salun alun, amma ba zai halarci taron mika ragamar mulki ga Joe Biden ba.
342/