ABNA24 : Shafin yanar gizo na labarai mai suna “Al-Ma’alumah” na kasar Iraki ya nakalto Ghiyath Surjii wani dan kungiyar hadakan kurdawan kasar Iraki yana fadar haka a yau Talata.
Surjii ya kara da cewa babu wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin kasar Iraki da kasar Turkiyya, dangane da samuwar sojojin kasar Turkiyya a cikin kasar Iraki.
Gwamnatin kasar Turkiyya dai ta fake da neman mayakan kungiyar PKK ta yantawayen kasarta, ta shigo yankin kurdawan kasar Iraki tana ayyukan leken asiri, da kuma kai hare-hare kan wasu wurare a wasu lokuta.
342/