ABNA24 : Shugaban hukumar zaɓen ƙasar Danny Lucas ne ya sanar da hakan a yayin da yake sanar da sakamakon zaɗen a jiya Lahadi inda ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa Mr. Ramkalawan shi ne ya lashe zaɓen.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa ɗan takaran jam’iyyar adawan Wavel Ramkalawan, wanda wannan shi ne karo na 6 yana tsayawa takarar shugaban ƙasar, ya sami kashi 54.9 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa alhali shi kuma shugaban ƙasar ya sami kashi 43.5 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa ɗin.
Hakan tana nufin za a kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar United Seychelles Party wacce take mulkin kasar tun shekarar 1977, da kuma shugabancin shugaba Faure din wanda yake mulkin ƙasar tun a shekara ta 2016.
342/