19 Oktoba 2020 - 12:47
Tawagar Kotun ICC Ta Isar Sudan Don Tattauna Batun Mika Mata Tsohon Shugaba Al-Bashir

Rahotanni daga kasar Sudan suna nuni da cewa tawagar kotun kasa da kasa mai shari’ar manyan laifuffukan yaki wacce ta isar kasar Sudan a jiya Asabar tana ci gaba da tattaunawa da mahukutan kasar kan yadda za a mika mata tsohon shugaban kasar Umar Hasan al-Bashir don yi masa shari’a kan laifuffukan yaki da ake zarginsa da su.

ABNA24 : A wata sanarwa da ofishin firayi ministan na Sudan Abdalla Hamdok ya fitar ya ce tawagar wacce take karkashin jagorancin babbar mai shigar da kara na kotun Malama Fatou Bensouda ta iso Sudan din ne tun jiya Asabar kuma za ta ci gaba da zama a Sudan din har zuwa ranar Laraba mai zuwa inda ake sa ran za ta tattauna da jami’an na Sudan dangane da irin hadin kan da gwamnatin Sudan din za ta bayar cikin shari’ar da ake son yi wa tsohon shugaba al-Bashir.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce wata majiya gwamnatin ta Sudan ta shaida masa cewa daga cikin abubuwan da bangarori biyu za su tattauna har da batun yadda za a mika wa kotun tsohon shugaba Al-Bashir din da kuma yadda za su tafi da shi kotun da ke birnin Hague don gurfana a gaban kotun bisa zargin kisan gilla da cin zarafin al’umma da ke masa a yayin rikicin Darfur na kasar a shekara ta 2003 da aka kiyasta cewa kimanin mutane 300,000 aka kashe.

Ana dai tsare da Al-Bashir din ne a wani gidan yari a garin Khartoum tun bayan da aka kifar da gwamnatinsa biyo bayan boren da al’umma suka yi.

Har ya zuwa yanzu dai gwamnatin Sudan ba ta fito karara ta bayyana cewa ko za ta mika Al-Bashir din ga kotun duniya din ba, to amma dai wasu alamu suna nuni da yiyuwar hakan.

342/