ABNA24 : A jiya Talata ce dai aka kada kuri’ar kan bukatar da Saudiyyan ta gabatar na shiga kwamitin inda ta sami kuri’u 90 kacal cikin kuri’u 193 da aka kada, lamarin da ya hana ta samun damar cikin cikin kwamitin.
Rashin nasarar da Saudiyyan ta fuskanta dai ya zo ne bayan da kungiyar nan ta kare hakkokin bil’adama ta Human Rights Watch ta bukaci shugabannin kasashen duniya da su kada kuri’ar rashin amincewa da wannan bukata ta Saudiyya saboda abin da ta kira ‘gagarumin take hakkokin bil’adama’ da Saudiyya ta yi kuma ta yi kaurin suna kan hakan.
Daga cikin abubuwan da aka yi ishara da su wajen kin amincewa da bukatar Saudiyyan har da ci gaba da hare-haren da take kai wa kasar Yemen da yayi sanadiyyar kashewa ko kuma raunana sama da kananan yara 7200, bugu da kari kuma kan kisan gillan da Saudiyyan ta yi wa sanannen dan jaridar kasar Jamal Khasoggi a kasar Turkiyya.
342/