9 Oktoba 2020 - 14:17
​Sudan: Jam’iyyar Ummah Ta Yi Watsi Da Duk Wani Batun Kulla Alaka Da Isra’ila

Jam’iyyar Umma a kasar Sudan ta bayyana hankoron da sabbin mahukuntan kasar ke yi na neman kulla alaka da yahudawan da cewa hakan ba zai haifar ma Sudan da mai ido ba.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na arabi21 cewa, jam’iyyar Umma a kasar Sudan ta bayyana cewa, kulla alaka da yahudawan da cewa hakan ba zai haifar ma Sudan da mai ido ba, maimakon haka ma sai matsaloli da hakan zai jawo mata.

Jam’iyyar Umma karkashin shugabancin Sadiqul Mahdi ta yi imanin cewa, dukkanin abin da Amurka take fadawa gwamnatin Sudan, magana ce ta siyasa, amma manufar hakan daban take daga abin da Sudan take tsammani.

Bayanin ya ce; idan Sudan ta mika kai ga yahudawan Isra’ila, hakan ba zai fitar da ita daga cikin matsalolinta ba, kuma alkawullan da aka yi mata ba za su tabbata ba, amma Amurka da Isra’ila za su iya cimma nasu burin ta hanyar sanya Suda ta yi hakan.

A cikin wanann makon ne Hamidati mataimakin shugaban majalisar mulki ta kasar Sudan ya bayyana cewa, an yi musu alkawalin cewa idan suka kulla alaka da Isra’ila, Amurka za ta cire sunan Sudan daga cikin masu daukar nauyin ta’addanci, kuma za a bunkasa ma kasar tattalin arzikinta, a kan haka a shirye suke su aiwatar da wanann bukata.

342/