ABNA24 : Shafin yanar gizo na labarai, AfricaNews ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba bu dan Afirka, sannan ba bu mace da ta taba rike mukamin shugaban kungiyar kasuwanci ta duniya.
Labarin ya kara da cewa ya zuwa jiya jumma’a dai, mutane 5 ne suka rage a cikin yan takara 8 masu neman kujerar, bayan janyewar yan takara guda ukku.
Daga cikin wadanda suka rage dai akwai Amina Muhammad na kasar Kenya da kuma Ngozi Okonja-Iweala na tarayyar Nigeriya sai kuma Yoo Myung-hee daga Korea ta Kuduk. Sai kuma a bangare maza akwai Liam Fox na kasar Burtaniya da kuma Mohammad Al-Tuwaijri na kasar Saudia.
An samar da kungiyar kasuwanci ta duniya WTO ne a shekara ta 1995 kuma tana da mambobi 163. A watan da ya gabata ne shugaban kungiyar Roberto Azevedo ya ajiye mukamin nasa kafin cikar wa’adi.
342/